Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa da Birtaniya za su yi maganin ma su fataucin bakin-haure

Kasashen Britaniya da Faransa sun sanya hannu kan wani sabon shirin yaki da ma su Fataucin bakin-haure ta Mashigin Calais, matakin da ke zuwa a dai-dai lokacin da matalar bakin haure ke sake zama babba barazana ga kasashen Turai.

Ministocin cikin gidan Faransa da Birtaniya Bernard Cazeneuve da Theresa May
Ministocin cikin gidan Faransa da Birtaniya Bernard Cazeneuve da Theresa May REUTERS/Regis Duvignau
Talla

Yarjejniyar da aka kulla karkashin ministan cikin gidan Britaniya Theresa May da takwaranta Bernard Cazeneuve na Faransa ta kunshi hadin kan kasashen biyu wajen tsaurara matakan tsaro a Mashigin Calais

Thareza ta ce Birtaniya da Faransa za su kara kaimin tsaro a yankunan Calais inda ‘yan cirani ke ratsowa daga Faransa domin tsallakawa zuwa Birtaniya.

Sannan za su Ci gaba da karfafa hadin gwiwar jami’an tsaronsu, wanda ya kunshi karo yawan ‘yan sanda, da na’urorin daukar hoto, tare da katange yankin na Calais.

Tattaunawar Ministocin biyu na zuwa ne bayan taron ‘yan ci-rani da aka gudanar a Berlin, inda aka amince a gudanar da babbar taro tsakanin Turai da Afrika a Malta a watan Nuwamban bana.

Yanzu haka gwamnatin kasar Macedonia ta kafa dokar ta-baci akan iyakarta da Girka domin hana kwararar bakin haure zuwa cikin kasar.

Yanzu haka dai akwai baki sama da dubu daya da 500 da suka taru kusa da iyakar kasar, inda aka tura dimbin jami’an tsaro domin hana su tsallakawa zuwa cikin kasar.

A cikin wannan mako dubban jami’an tsaro ne suka kutsa a cikin kasar Girka, lura da yadda aka kange tsohuwar hanyar Italiya da bakin hauren suka saba amfani da ita.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.