Isa ga babban shafi
Birtaniya

Bai kamata a kambama harin London ba-May

Firaministar Birtaniya Theresa May ta kalubalanci kalaman shugaban Amurka Donald Trump dangane da kambama harin Bom din layin dogon karkashin kasar da ya faru a birnin London da safiyar yau. Hukumomi dai a kasar basu sanar da mutuwar ko da mutum guda sanadiyyar harin ba, illa mutum 22 da suka jikkata.

Firaministar Birtaniya Theresa May.
Firaministar Birtaniya Theresa May. Reuters
Talla

A cewar Theresa May wadda ke mayar da martini kan sakon Twitter da Donald Trump ya aike mata, bai kamata a rika kambama harin ba, ganin cewa ana ci gaba da bincike kuma da zarar an kammala za a sanar da manema labarai gaskiyar abin da aka gano.

Sai dai a bangaren Trump, cewa ya yi ya so ya kira, Theresa May tun da safiyar yau don jajanta mata a harin daya ce an shirya shi ne don haddasawa birnin tarin matsaloli.

Hukumomi dai a Birtaniya sun ce babu alamun rasa ran ko da mutum guda sanadiyyar harin face wadanda suka jikkata mutum 22 kuma suma mutum 18 ne kadai ke karbar kulawa a asibiti yayinda hudun da suka samu raunuka suka wuce zuwa wajen ayyukansu.

Harin Bom din dai ya faru ne da safiyar yau Juma’a a dai dai lokacin mutane da dama ke gaggawar isa wuraren ayyukansu.

Yanzu haka dai jami’an ‘yan sandan birnin na London na gudanar da bincike kan fashewar inda kuma suke kallon lamarin a matsayin yunkurin harin ta’addaci.

Tuni dai Magajin garin birnin na London, Sadiq Khan ya bukaci jama’a da su kwantar da hankukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.