Isa ga babban shafi
Amurka

Irma: 'Tilas karin mazauna Florida 700,000 su fice daga gidajensu'

Gwamnatin Amurka ta bada umarnin cewa yawan mazauna jihar Florida da ya zama tilas su fice daga gidajensu ya kai miliyan 6 da dubu 300, daga miliyan 5 da dubu 600, kamar yadda ya ke a baya.

Wasu daga cikin dubban mazauna jihar Florida da suka kauracewa gidajensu domin kaucewa guguwar Irma. Mutanen sun yi jerin gwano a gaban wani gini da aka tanada don irin wannan rana. 9 ga Satumba 2017.
Wasu daga cikin dubban mazauna jihar Florida da suka kauracewa gidajensu domin kaucewa guguwar Irma. Mutanen sun yi jerin gwano a gaban wani gini da aka tanada don irin wannan rana. 9 ga Satumba 2017. REUTERS/Bryan Woolston
Talla

Matakin da jami’an ceto suka tabbatar na nufin cewa tilas karin mazauna jihar ta Florida dubu 700,000, su fice, domin kaucewa halaka daga kakkarfar guguwar Irma da ke dada tunkaro su.

Tuni kakkarfar guguwar ta Irma, da ta yi gagarumin ta’adi a yankin Caribbean, ta isa yankin arewa maso gabashin kasar Cuba, dauke da mamakon ruwan sama, da iska mai karfin gaske, a mataki na 5.

Sai dai masana, sun tabbatar da cewa karfin guguwar ta Irma ya ragu zuwa mataki na 4, bayan da ta isa Cuban da safiyar yau Asabar.

A baya dai guguwar na sharara gudun kilomita kusan 300 ne a sa’a guda, amma a yanzu ta koma gudun kilomita 249 a sa’a daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.