Isa ga babban shafi
Amurka-Faransa

Guguwar Irma ta yi mummunan ta'adi a Caribbean da Amurka

Guguwar Irma da ke dauke da ruwan sama mai karfi, ta kashe akala mutane 10 tare da lalata dukiya mai tarin yawa a kasashen yankin Caribbean, inda a halin yanzu ta doshi Amurka.

Tsibirin Saint-Martin mallakin Faransa, wanda guguwar Irma ta shafa a watan satumbar 2017
Tsibirin Saint-Martin mallakin Faransa, wanda guguwar Irma ta shafa a watan satumbar 2017 RCI GUADELOUPE/REUTERS
Talla

Mutane akalla milyan daya da dubu 200 ne wannan guguwa ta shafa kamar yadda alkaluman kungiyar agajin kasa da kasa ta Red Cross suka nuna, kuma ga alama guguwar wadda ke ci gaba da shafar kasashen Caribbean da kuma wasu jihohi na Amurka za ta iya haddasa barnar da yawanta za ta kai ta dala bilyan 120.

A tsibirin St Martin sama da kashi 60 cikin dari na gidaje da gine-gine ne ta shafa, yayin da a tsibirin Barbuda kawai ta shafi sama  kashi 30 cikin dari na al’ummar da ke rayuwa a can kamar dai yadda hukumar hasashen yanayi da ke Miami a Amurka ta bayyana.

Tuni dai guguwar ta isa kasashen yankin arewacin Amurka, inda take gudun kilomita 295 a kowace sa’a lokacin da ta isa kasar Puerto Rico, kuma tuni mutane biyu suka rasa rayukansu a can, yayin da wasu hudu suka mutu a tsibirin Virgin Islands wanda mallakin Amurka ne.

Irma, wadda masana suka bayyana a matsayin guguwa mafi  karfi da kuma gudu a cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan, za ta ci gaba da shafar kasashen yankin har zuwa gobe asabar kafin watakila gudunta ya dawo zuwa kilomita 175 a ciki sa’a daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.