Isa ga babban shafi
Amurka

Kakkarfan ruwan sama a Texas ya kawo nakasu a ayyukan ceto

A daidai lokacin da ma’aikatan agaji ke ci gaba da aikin ceto a jihar Texas da ke Amurka, wani ruwan sama mai karfin gaske ya sake dawowa a yankin, inda ya kara haddasa cikas ga masu ayyukan ceton.

A wannan karo dai guguwar ta fi shafar gagaruwan da ke gabar ruwan gabashin Amurka ne
A wannan karo dai guguwar ta fi shafar gagaruwan da ke gabar ruwan gabashin Amurka ne Reuters
Talla

Ruwan sama mai karfin gaske ne ya sake dawowa a yankin bayan share tsawon kwanaki biyar ana gudanar da aikin ceto sakamakon ambaliyar ruwan wadda ta samu asali daga mahaukaciyar guguwar nan mai suna Harvey.

A wannan karo dai guguwar ta fi shafar gagaruwan da ke gabar ruwan gabashin Amurka ne, kuma birnin Houston na jihar Texas da kuma Lousiana da ke Orleans, na daga cikin wadanda ambaliyar ta fi yin mumman ta’adi.

Duk da cewa kawo yanzu ba wasu cikakkun alkaluma dangane da adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon wannan lamari, da ke gaf da share tsawon mako daya, to amma kafafen yada labarai na Amurka na cewa adadin mamatan zai kai 30.

Akwai mutane kusan milyan daya da suka bar gidajensu, yayin da wasu da dama suka makale a wasu yankuna sakamakon yadda ruwa ya yanke hanyoyin mota, turakun wutar lantarki da na wayar tarho, kamar dai yadda Brock Long na hukumar agajin gaggawa a jihar Texas ya bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.