Isa ga babban shafi
Amurka

Guguwa mai gudun kilomita 195 a sa'a guda ta afkawa Texas

Mahaukaciyar Guguwa mai karfin gaske, ta afkawa jihar Texas da ke Amurka, wadda masana suka bayyana ta a matsayin babbar masifa ga jihar da ma makwabtanta.

Wasu mutane a yankin Corpus Christi da ke jihar Texas, yayinda suke kokarin gujewa guguwar Harvey mai karfin gaske da ta afkawa yankinsu.
Wasu mutane a yankin Corpus Christi da ke jihar Texas, yayinda suke kokarin gujewa guguwar Harvey mai karfin gaske da ta afkawa yankinsu. REUTERS/Adrees Latif
Talla

Guguwar mai tafiyar kilomita 195 a sa’a guda, da masana suka yi wa lakabi da Huriccane Harvey, ana sa ran ta zama mafi karfin wadda ta taba afkawa Amurka tun bayan makamancin hakan a shekarar 2005.

Tun kafin guguwar ta isa jihar, shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan takardar ayyana Texas a matsayin jihar da ke fuskantar masifa, tare da bada umarnin fitar da kudaden kai agaji.

An dai samu katsewar wutar lantarki a mafi yawancin sassan jihar, yayin da guguwar ke tunkarota, kuma ana sa rana ta juye ruwan sama kan ma’aunin Senti mita 89 tsawon kwani hudu zuwa biyar a sassan jihar ta Texas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.