Isa ga babban shafi
Faransa

Attajirin Faransa Pierre Bergé ya rasu yana da shekaru 86

Shahrarren dan kasuwar Faransa Pierre Bergé, wanda kuma ya shahra sakamakon bayar da dukiyarsa don gudanar da ayyukan jinkai a sassan duniya, ya rasu a wannan juma’a yana da shekaru 86, bayan da ya share tsawon shekaru yana jinya.

Pierre Bergé, shahrarren dan kasuwa kuma mai jinkai a Faransa,
Pierre Bergé, shahrarren dan kasuwa kuma mai jinkai a Faransa, AFP/Stephane de Sakutin
Talla

Pierre Berge, wanda babban amini ne ga mai kamfanin dinka tufafin kasaita nan da ya yi suna a duniya wato Yves Saint Laurent, ya rasu ne ana sauran makonni kadan a kaddamar da wasu cibiyoyin ajiye kayayyakin tarihi masu nasaba da tarihin dinka tufafi guda biyu a kasar.

Ko baya ga kafa gidauniya da ke taimakawa da makuddan kudade domin yaki da cutar kanjamau a duniya, Pierre Berge na da hannayan jari a wasu kamfanoni da suka hada da jaridar Le Monde, yayin da ya kasance amini na kut-da-kut ga tsohon shugaban kasar Francois Mitterand.

Alkalumman sun tabbatar da cewa kadarorin da Berge ya mallaka shi kadai, da kuma wadanda ke cikin kamfanonin hadin-guiwa tsakaninsa da sauran abokannin kasuwancinsa, sun haura Euro milyan 200.

A shekarar 1994 ne Pierre Berge ya kafa kungiyar yaki da cutar kanjamau da ake kira Essemble conte le Sida, kafin daga bisani kungiyar ta canza suna zuwa Sidaction.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.