Canjin yanayi ya sauya lokacin samun ambaliyar ruwa a Turai
Wani binciken masana ya nuna cewar canjin yanayi ya sauya lokacin da ake samun ambaliyar ruwa a Turai, inda ake samun wasu koguna na cika da wuri, wasu kuma a makare, abinda ke matukar illa ga ayyukan noma da rayuwa baki daya a Yankin.
Wallafawa ranar:
Rahotan binciken da aka wallafawa a Mujallar Kimiya ta Amurka, shine mafi girma da aka taba yi a Turai wanda ya dauki shekaru 50 wajen tattara bayanai daga tashoshin bincike sama da 4,000 a kasashe 38.
Farfesa Guenter Bloeschi na Jami’ar Fasaha ta Virginia da ya jagoranci binciken, ya ce a kasashe irin su Sweden da Findland da Yankin Baltic, a kan samu ambaliya wata guda kafin yadda aka saba gani a shekaru 1960 da 1970.
Shehun malamin ya ce a wancan lokacin a kan samu matsalar ce a watan Afrilu, amma a yau ana samu ne a watan Maris saboda narkewar dusar kankara da wuri.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu