Isa ga babban shafi
Faransa

Calais: Kotu ta goyi bayan bakin haure

Wata kotun Faransa ta umurci gwamnatin kasar, da ta taimaka wa bakin haure da aka kora daga wani sansani da ake kira Calais kusa da iyakar kasar da Birtaniya tun cikin watan oktoban bara.

Sansanin bakin haure na Calais da ke kan iyakar Faransa da Birtaniya
Sansanin bakin haure na Calais da ke kan iyakar Faransa da Birtaniya Philippe Wojazer / Reuters
Talla

Sai dai kotun ba ta ce a sake bude wannan sansani ba kamar yadda wasu kungiyoyin kare hakkin bil’adama suka bakata.

Kotun da ta yi zamanta a birnin Lille da ke arewacin Faransa, ta bai wa gwamantin kasar kwanaki 10, domin fara aiwatar da wannan umurni, idan kuma ta gaza aiwatar da shi za a ci ta tarar Euro 100, a kowace rana.

Daga cikin abubuwan da kotun ta umurci a yi wa bakin hauren sun hada da samar da ruwan sha da kuma makewayi ga akalla bakin da yawansu ya kama daga 400 zuwa 600 a matakin farko, wannan kuwa lura da yadda suke rayuwa a yanayi na rashin tsafta.

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama 11 ne a Faransa suka shigar da wannan kara a ranar larabar da ta gabata, bayan da mahukunta suka dakatar da agajin abinci da ake raba wa bakin, wadanda mafi yawansu sun fito ne daga kasashen Afirka da kuma Asiya.

Wasu daga cikin abubuwan da kungiyoyin suka bukaci kotun ta birnin Lille ta umurci gwamnatin Faransa, sun hada da tilasta ma ta kafa wata cibiya da za ta kunshi gidajen kwana na dindindin a garin na Calais saboda ‘yan ci-rani, matakin da kotun ta yi watsi da shi.

Akalla mutane 7.000 ne aka kora daga wannan sansani a cikin watan oktoban shekara ta 2016 da ta gabata bayan samun umurnin wata kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.