Isa ga babban shafi
Birtaniya

'Yan Sandan Birtaniya na tsare da mutane 12 saboda harin ta'addanci da wuka

Firaministan Birtaniya Uwargida Theresa May ta danganta harin ta'addanci da wasu suka kai da wukake daren jiya a London da cewa tsatstsauran hakida ya kai ga harin, inda suka kashe mutane bakwai.

Wasu 'yan sanda na sintiri a tsakiyar London watan jiya.
Wasu 'yan sanda na sintiri a tsakiyar London watan jiya. REUTERS/Neil Hall
Talla

'Yan sanda  sun bayyana cewa suna tsare da mutane 12 sakamakon wancan hari.

Harin na jiya an kai shi ne a daidai Gadan London indajama'a ke hada-hada da dare.

Bayanai na nuna mutane uku suka fito daga cikin wata mota sanye da wasu abubuwa kamar jigidan harin kunar bakin wake sannan suka yi ta farma mutane da sara da suka da wukake.

Wannan hari ya kasance na uku kenan a Birtaniya cikin watanni uku.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.