Isa ga babban shafi
Birtaniya

Majalisar Birtaniya ta amince a gudanar da zaben gaggawa

Majalisar birtaniya ta amince da gagarumin rinjaye kan bukatar Firaminista Tharesa May da ta ti kira zaben gaggawa a 8 ga watan Yuni. ‘Yan majalisa 522 suka amince yayin da 13 suka kada kuri’ar kin amincewa.

Firaministar Birtaniya Theresa May na son a gudanar da zaben game-gari a ranar 8 ga watan Juni mai zuwa
Firaministar Birtaniya Theresa May na son a gudanar da zaben game-gari a ranar 8 ga watan Juni mai zuwa REUTERS/Toby Melville
Talla

Kudirin Firaministar na bukatar samun goyon bayan kashi biyu cikin uku na ‘yan Majalisar kafin amince wa da shi, yayin da Jeremy Corbyn na jam’iyyar Labour mai adawa ya yi marhaba da bukatar May.

May na neman gagarumin rinjaye musamman a Majalisar Dokoki kan bangaren ‘yan adawa gabanin ficewar kasar daga Tarayyar Turai.

Firaministar ta ce, tana bukatar samun goyon al’ummar Birtaniya kan yarjejeniyarta ta ficewa daga kungiyar kasashen Turai.

A wata hira da ta yi da jaridar Sun,  May ta ce, rudanin sisyasa na barazana ga ci gaban tattaunawar ficewar Birtaniya, yayin da ta zargi ‘yan adawa da haifar ma ta da cikas a yunkurinta.

Da farko dai, an shirya guadanar da zaben game garin Birtaniya a shekarar 2020, amma dokar kasar ta bada damar kawo zaben kusa kusa, matukar hakan ya samu goyon bayan kashi biyu bisa uku na ‘yan Majalisa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.