Isa ga babban shafi
Faransa

Kalubalen da ke gaban Macron

Akwai manyan kalubale da ke gaban Emmanuel Macron shugaban Faransa mai jiran gado, bayan ya doke Marine Le Pen mai tsattsauran ra’ayi a zaben shugaban kasa zagaye na biyu da aka gudanar a ranar Lahadi.

Shugaban Faransa mai jiran gado Emmanuel Macron
Shugaban Faransa mai jiran gado Emmanuel Macron Patrick KOVARIK / AFP
Talla

Macron ya samu sama da kashi 66 na kuri’un da aka kada abinda ya ba shi nasarar kan Marine Le Pen da ta samu sama da kashi 35.

Kalubalen da ke gaban Macon sun hada da samun rinjaye a Majalisa

Babban kalubalen da ke gaban shugaban mai jiran gado shi ne samun rinjaye a zaben majalisar dokokin Faransa da za a gudanar a watan gobe domin aiwatar da alkawullan da ya dauka.

Macron zai fuskanci kalubale a zaben ‘Yan Majalisu daga manyan jam’iyyun siyasa musamman jam’iyyar Republican da dan takararta Francois Fillon ya sha kaye a zagaye na farko da kuma jam’iyyar Socialist da shugaba Hollande.

Hada kan Faransawa

Wani kalubale da ke gaban Emmanuel Macron shi ne hada kan Faransawa musamman yadda zaben kasar na bana ya raba ‘yan kasar.

Macron sai ya yi kokarin hada kan Faransawa musamman magoya bayan manyan jam’iyyun siyasar Faransa da suka sha kaye da kuma wadanda suka marawa ‘yan takara masu tsattsauran ra’ayi baya.

Wasu Faransawa da dama sun zabe shi ne domin tabbatar da ganin an kada Marine Le Pen mai tsatsauran ra’ayi.

Rashin ayyukan yi

Magance matsalar ayyukan yi na daga cikin manyan kalubalen da Macron zai fuskanta, musamman alkawullan da ya dauka na sanin hanyoyin kawo karshen matsalar.

Ma’aunin matsalar rashin ayyukan yi a Faransa ya kai kashi 10.

Macron ya sha alwashin magance matsalar rashin ayyukan yi da kashi bakwai zuwa shekarar 2022, ta hanyar samar da sabbin tsare tsaren aikin kwadago a kasar.

Barazanar ta'addanci

Batun kawo karshen barazanar ta’addanci a Faransa da ma Turai zai kasance babban kalubale a gaban Macron.

Tun 2015 Faransa ke fuskantar barazanar hare haren ta’addanci inda mutane sama da 230 suka mutu a harin da kungiyar IS ta kai a Paris.

Macron zai fuskancii kalubalen sake tsara Tarayyar Turai musamman ficewar Birtaniya da matsalar ‘yan gudun hijira.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.