Isa ga babban shafi
Faransa

Shugabannin duniya sun taya Macron murna

Shugabannin Kasashen duniya sun taya Emmanuel Macron murnar lashe zaben shugaban kasar Faransa zagaye na biyu da aka gudanar a ranar Lahadi inda ya doke abokiyar hammayar shi Marine Le Pen mai tsattsauran ra’ayi.

Shugaban Faransa mai jiran gado Emmanuel Macron
Shugaban Faransa mai jiran gado Emmanuel Macron REUTERS/Christian Hartmann
Talla

Shugaban Amurka Donald Trump ya taya Macron Murna tare da bayyana fatar yin aiki tare da sabon shugaban.

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce nasarar Macron nasara ce ta hadaddiyar Turai da kuma dangantakar da ke tsakanin Faransa da Jamus.

Firaministar Birtaniya Theresa May ta bayyana Faransa a matsayin babbar kawar Birtaniya, inda ta bayyana aniyar yin aiki tare da sabon shugaban na Faransa Emmanuel Macron mai jiran gado.

Shuagban gudanarwar kungiyar kasashen Turai, Jean Claude Juncker ya bayyyana nasarar Macron a matsayin abinda zai tabbatar da dorewar kungiyar.

A nasa bangaren shugaban Tarayyar Turai Donald Tusk ya ce Faransawa sun zabi ‘yanci da daidaito da kuma hadin kai, saboda haka yana taya su murna.

Sauran wadanda suka aike da sakon taya murna sun hada da shugaban China, Xi Jinping da Firaministan Japan Shinzo Abe da Firaministan Canada Justin Tradeau da Firaminsitan Australia, Malcolm Turnball da na Girka Alexis Tspiras da sauran shugabannin duniya da suka da Hillary Clinton da ta sha kaye a zaben Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.