Isa ga babban shafi
Faransa

Macron ya shigar da karar zargin da Le Pen ta yi

Yayin da ya rage kwanaki biyu a gudanar da zaben shugaban kasar Faransa zagaye na biyu, Emmanuel Macron ya shigar da kara kotu inda ya ke bukatar gudanar da bincike kan zargin da abokiyar hamayyarsa Marine Le Pen ta yi kan cewar ya mallaki asusun ajiya a kasashen waje.

Emmanuel Macron da Marine Le Pen yan takarar shugaban kasa a zaben Faransa
Emmanuel Macron da Marine Le Pen yan takarar shugaban kasa a zaben Faransa REUTERS/Eric Feferberg/Pool
Talla

Tuni dai ofishin mai gabatar da kara ya sanar da fara binciken.

Le Pen ‘yar ra’ayin rikau ta yi zargin ne a lokacin da suke fafatawa a muhawara a ranar Laraba inda ta ce Macron ya mallaki wani asusun ajiya a Bahamas.

Le Pen dai na kokarin datss yawan gibin da Macron ya ba ta inda kuri’un jin ra’ayin jama’a ke ci gaba da nuna za ta sha kaye a zagaye na biyu da al’ummar Faransa za su kada kuri’a a ranar Lahadi.

Abdulkarim Ibrahim Shikal da ke sa ido ga siyasar Faransa ya aiko da rahoto daga Paris.

01:06

Macron ya shigar da karar zargin da Le Pen ta yi

Abdoulkarim Ibrahim

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.