Isa ga babban shafi
Faransa

Paris: ‘Yan sanda sun yi arangama da masu zanga-zanga

Hukumar ‘Yan Sandan Faransa ta ce jami’anta guda biyu sun jikkata lokacin da aka samu arangama tsakaninsu da matasan da ke zanga-zangar ranar ma’aikatan kwadago da ke zuwa kwanaki 6 a gudanar da zaben shugaban kasar.

Zanga-zangar kungiyoyin kwadago a Paris
Zanga-zangar kungiyoyin kwadago a Paris REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Rahotanni sun ce, matasan da suka rufe fuskokinsu sun yi ta jifar ‘Yan Sanda wadanda suka mayar da martani da hayaki mai sa hawaye.

‘Yan sandan kuma sun yi amfani da harsasan roba domin tarwatsa masu zanga-zangar sama da 200.

Zana zangar dai ta samo asali ne daga jerin gwanon al’ada na kungiyoyin kwadago da ake gudanarwa 1 ga Mayu duk shekara.

Masu zanga-zangar a Paris sun fito rike da da kyallayen da ke dauke da sakwannin rashin jin dadi kan koma bayan ci gaban rayuwa mai inganci a kasar, da kuma nuna kyama ga jam’iyar masu tsatsauran ra’ayi ta Marine Le Pen da ke shirin fafatawa da Emmanuel Macron dan takara mai zaman kansa a ranar 7 ga Mayu

Za a iya cewa dai kanun kungiyoyin kwadagon da suka gudanar da jerin gwanon na yau litanin sun rabu dangane da kiran kauracewa zaben Marine Le Pen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.