Isa ga babban shafi
Faransa

Faransawa na bayyana damuwarsu kan zaben kasar

Rahotanni daga kasar Faransa na nuna cewar, al’ummar kasar da dama na bayyana damuwar su kan 'yan takarar shugabancin kasar da za su je zagaye na biyu, Marine Le Pen da Emmanuel Macron.

Hotunan 'yan takaran Zaben Faransa Emmanuel Macron da Marine Le Pen
Hotunan 'yan takaran Zaben Faransa Emmanuel Macron da Marine Le Pen REUTERS/Robert Pratta
Talla

Wani bincike ya ce 7 cikin mutane 10 basu gamsu da ingancin ‘yan takaran ba, yayin da ‘yan takarar manyan Jam’iyyun kasar biyu suka kasa kai gaci.

Zanga zangar da aka yi wadda ta haifar da arangama tsakanin matasa da ‘yan Sanda ranar 1 ga watan Mayu, ya dada fito da rashin amincewar jama’a game da ‘yan takaran biyu, yayin da wasu Magoya bayan Luc Melenchon suka ce su ba zasu kada kuri’a ba.

Shi kuwa tsohon dan takarar shugabancin kasar Francois Fillon ya ce labarin da aka wallafa akan sa na samarwa iyalan sa ayyuka na bogi ya yi matukar tasiri wajen faduwar sa zaben shugaban kasar zagayen farko.

Korafin Fillon ya mayar da hankali ne kan labarin da Mujallar Le Canard Enchaine ta wallafa wanda ya zargi tsohon Firaministan da biyan iyalan sa ba tare da gudanar da aiki ba.

Tuni dai hukumomi suka kaddamar da bincike akan dan takarar inda aka gurfanar da shi a gaban kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.