Isa ga babban shafi
Turkiya

Erdogan ya sake korar ma'aikata dubu 40

Gwamnatin kasar Turkiya ta sake korar dubban ma’aikata daga bakin aiki sakamakon zarginsu da hada kai da babban dan adawar kasar mai gudun hijira. A wannan karon ma’aikata dubu 40.00 ne aka kora daga bakin aiki bayan da gwamnati ta zarge su da goyon bayan shehin malamin nan Fethullah Gülen, mutumen da ake zargi da shirya juyin mulkin da bai cimma nasara ba a kasar.  

Taron gangamin makiya gwamnatin Turkiya  17 afrilu 2017.
Taron gangamin makiya gwamnatin Turkiya 17 afrilu 2017. REUTERS/Kemal Aslan
Talla

A jimilce dai za a iya cewa, tun daga yinkurin juyin mulkin kawo yau watanni 9 ke nan, ma’aikata dubu 120 ne gwamnatin Turkiya ta kora daga bakin aiki, al’amarin dake nuna cewa, har yanzu shugaba Erdogan kasar bai huce ba, kuma baya da niyar kawo karshen bita da kullin da take yiwa magoya Fethullah Gülen, dake gudun hijira a kasar Amruka.

A dai gefen kuma, Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya nuna bacin ransa kan sintirin da mutocin dakarun kasar Amruka ke yi a yankin kan iyakarta da kasar Syriya, tare da mayakan sa kan kurdawa na kungiyar YPG, kungiyar da Turkiya ke kallo a matsayin ta yan ta’adda.

hadadiyar kungiya radakarun kare demokradiya a kasar Syriya (FDS), ta hadin guiwar Kurdawa da Larabawa dake yakar kungiyar dake ikrarin jihadi ta Isis, tare da goyon bayan kasar Amruka

Ita dai Turkiya na daukar wannan kungiya ta kurdawa ne a matsayin wani reshen kungiyar ‘yan awaren Kurdawa ta PKK dake cikin kasar Syriya.

Ita dai kungiyar yan awaren Kuradawa ta PKK dake tafka kazamin fada, da dakarun Turkiya tun a cikin shekarar 1984 turkiya da wasu kawayenta na yammaci ke daukarta a matsayin kungiyar yan ta’adda.

A cikin wannan makon da muke ciki ne dakarun Turkiya suka kaddamar da wasu jerin hare haren jiragen sama a kan sananin mayakan kungiyar ta YPG, dake arewa maso gabashin Syriya, inda ta kashe mayaka 28, a yayinda aka samu wasu jerin fadace fadace tsakanin bangarorin biyu a yankin kan iyakarta da Syria.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.