Turkiya ta hana amfani da Wikipedia
Turkiya ta datse shafin Wikipedia a kasar kan wani labarin da ya wallafa kan alakar gwamnatin Ankara da kungiyoyin ‘yan ta’adda.
Wallafawa ranar:
Hukumar sadarwar kasar ta ce ta haramta shafin da mutane da dama ke bincike labarai, sai dai babu cikaken bayani kan dalili.
Kafafan yadda labaran kasar sun ce haramci kan shafin ya biyo bayan gaza cire wani labari da ke talata ta’addanci da kuma tuhumar Turkiya da aiki tare da kungiyoyin ta’addanci.
Tuni dai kungiyoyi kare hakkin bil'adama suka soma sukar wannan haramci da suka bayyana cewa za yi tasiri ga rayuwar mutane da dama a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu