Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiya ta kawo karshen ayyukan sojinta a Syria

Kasar Turkiya ta sanar da kawo karshen ayyukan sojinta na fafata yaki a arewacin Syria domin murkushe mayakan ISIS.

Firaministan Turkiya Binali Yildirim yayin jawabi ga manema labarai a arewacin kasar Cyprus.
Firaministan Turkiya Binali Yildirim yayin jawabi ga manema labarai a arewacin kasar Cyprus. REUTERS/Yiannis Kourtoglou
Talla

Majalisar tsaron Turkiya, dake karkashin shugaban kasar, Recep Tayyip Erdogan ta sanar da samun gagarumar nasara a watanni shida da tayi tana kai hari kan mayakan cikin kasar Syria.

Firaministan Binali Yildrim wanda ya tabbatar da kawo karshen matakin sojin, yace duk da haka, nan gaba idan hali yayi suna iya komawa ci gaba da kai hare haren kan IS.

A watan Agustan shekarar da ta gabata ne Turkiya ta kaddamar da yaki kan mayakan Kurdawa da ta dauka a matsayin ‘yan ta’adda da kuma ‘yan kungiyar IS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.