Turkiya- Amurka
Turkiya ta zargi Amurka da taimakawa mayakan kurdawa YPG
Gwamnatin Turkiya ta zargi rundunar sojin Amurka da taimakawa mayakan kurdawa na YPG, wadanda ke neman yancin ballewar daga yankin kurdawan da ke Turkiya.
Wallafawa ranar:
Talla
Turkiya dai na kallon Kungiyar YPG a matsayin reshen kungiyar PKK da ta ke dauka a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.
An dai jima ana kai ruwa rana tsakanin Amurka da Turkiya bisa wannan zargi.
Sai dai a yanzu Turkiya na fatan bayan fara aikin zababben shugaban Amurka Donald Trump, ya janye taimakon da kasar ke bai wa mayakan Kurdawan na YPG da ke da alaka da jam’iyyar adawar kasar ta PYD.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu