Isa ga babban shafi
Turkiya

An kame 'yan jam'iyyar HDP 235 a Turkiya

Gwamnatin Turkiya ta kame mutane 235 daga Jam’iyyar HDP ta Kurdawa, saboda zargin alakarsu da kungiyar ‘yan tawayen PKK, a wani sumame da jami’an tsaro suka kaddamar fadin kasar.

Harabar filin wasan kwallon kafa na birnin Istanbul da aka kai harin bam
Harabar filin wasan kwallon kafa na birnin Istanbul da aka kai harin bam REUTERS/Murad Sezer
Talla

Kamen na zuwa ne kwananki biyu, bayan wani harin bam da aka kai a harabar filin wasan kwallon kafa na babban birnin kasar Istanbul, da ya hallaka mutane 44.

 

 

 

Ma’aikatar cikin gidan Turkiya ta yi karin bayanin cewa jami’an tsaron, sun gudanar da wannan sumamen ne a tsakanin larduna 11, da ke arewa maso yammaci da kuma kudu maso gabashin kasar.

A wani jawabi daya gabatar, yayin duba wadanda suka samu raunuka a harin da aka kai, ministan cikin gidan Turkiya Suleyman Soylu ya lashi takobin shafe wadanda ke da hannu cikin harin, wanda wani reshe na kungiyar ‘yan tawayen Kurdawa ta PKK sukai ikirarin kaishi.

Akalla jami’an ‘yan sandan kasar 36 ne suka rasa rayukansu daga cikin 44 a harin bam din da aka kai a harabar filin kwallon kafa da ke Istanbul.

A wani matakin martani, jiragen yakin Turkiyya sun yi barin wuta a yankunan da ke karkashin kungiyar PKK da ke arewacin Iraqi inda suka lalata shelkwatar kungiyar.

Kungiyar Kurdawa ta PKK da ta dauki makamai domin yakar gwamnatin Turkiya bisa neman yancin cin gashin kai a tun a shekara ta 1984, Gwamnatin Turkiya, tarayyar Turai dama majalisar Dinkin Duniya na daukarta a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.