Isa ga babban shafi
Faransa

Emmanuel Macron dan takarar zaben Faransa na 2017

Emmanuel Macron na daya daga cikin manyan ‘yan takara 11 a zaben shugaban kasa da za a gudanar a Faransa a ranar 23 ga watan Afrilu. Mun diba tarihinsa rayuwarsa kamar sauran ‘Yan takarar shugabancin na Faransa.

Dan takarar shugabancin Faransa Emmanuel Macron
Dan takarar shugabancin Faransa Emmanuel Macron RFI/Romain Ferre
Talla

Tarihin Emmanuel Macron

An haifi Emmanuel Jean Michel Frederic Macron a ranar 21 ga watan Disamban shekarar 1977 a Amiens da ke arewacin Faransa, kuma ya yi karatun digiri na farko a fannin Falsafa a jami’ar Nanterre a birnin Paris.

Ya kasance mamba a jam’iyyar Socialist tsakanin shekarar 2006 zuwa 2009, inda aka nada shi a matsayin babban magatakardar jam’iyyar a lokacin gwamatin Francois Hollande ta farko, wato a shekarar 2012, kafin daga bisani ya rike mukamin Minisatan tattalin arzikin da masana’antu a shekarar 2014.

Macron mai shekaru 39 ya yi murabus daga mukamnin siyasa a bara don kaddamar da shirinsa na tsayawa takara a zaben 2017.

A ranar 16 ga watan Nuwamban bara ne, Macron ya ayyana manufarsa ta neman maye kujerar shugaba Francois Hollande, bayan an dauki lokaci ana dakon sanar da haka.

A halin yanzu dai, Macron na daya daga cikin wadanda ake hasashen za su iya lashe zaben da za a gudanar a karshen mako, kuma shi ne mafi karancin shekaru daga cikin ilahirin ‘yan takara 11.

Macron ne daya daga cikin ‘yan takarar da ba shi da wata kwarewa wajen gwagarmayar yakin neman zabe.

A shekarar 2007 ne, Macron ya auri malamarsa da ta koyar da shi a babbar makaranta, wato Brigitte Trinye Trognuex kuma ta ba shi tazarar shekaru 24.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.