Isa ga babban shafi
Faransa

Melechon ya samu tagomashi a yakin neman zabensa

Biyu daga cikin jiga-jigan ‘yan takara a zaben shugabancin Faransa, Francois Fillon da Jean Luc Melechon sun gudanar da gagarumin yakin neman zabe a kokarinsu na ganin sun samu karin tagomashi daga magoya bayansu, yayin da zagayen farko na zaben  zai gudana a ranar 23 ga wannan wata na Aprilu.

Dan takarar shugabancin Faransa Jean-Luc Mélenchon a Maerseille
Dan takarar shugabancin Faransa Jean-Luc Mélenchon a Maerseille REUTERS/Jean-Paul Pelissier
Talla

An dai dauki tsawon makwanni kuri’ar jin ra’ayin jama’a na nuna dan takara mai zaman kansa Emmanuel Macron da mai ra’ayin kishin kasa Marine Le Pen a matsayin wadanda ke kan gaba wajen samun mogya baya tsakanin ‘yan takara 11 da za su fafata a zaben shugabancin kasar.

To sai dai kuma wani sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka fitar a baya-bayan nan nuna cewa Macron da Le pen a yanzu na fuskantar kalubale idan aka yi la’akari da tagomashin da dan takara Jean Luc Melenchon ke samu, in da a yanzu ya samu karin magoya baya da kashi 4 zuwa kashi 19, dai dai da tsohon Firaministan kasar kuma dan takara a yanzu wato Francois Fillon, wanda tauraruwarsa ta dusashe sakamakon bincikensa da ake bisa zargin biyan matarsa Penelope Fillon makudan kudade a matsayin albashi da ba ta cancanci karbarsu ba, sai kuma batun daukar ‘ya‘yansa masu karancin shekaru aiki a lokacin da ya ke rike da mukamin Firaminsta, matakin da ya saba wa dokar Faransa.

A wani lamarin kuma da masu iya magana kan ce ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare, wasu daga cikin masu sharhi na da ra’ayin cewa ya yi wuri a iya hasashen wanda ka iya lashe zagayen farko a zaben shugabancin Faransa, idan aka yi la’akari da sakamakon wata kuri’ar jin ra’ayi da aka fitar a watan da ya gabata da ke nuna har yanzu kashi 38 daga cikin al’ummar kasar ba su bayyana dan takarar da suke mara wa baya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.