Isa ga babban shafi
Faransa

Zaben Faransa: Kananan ‘yan takara na farin jinni

Wadanda ake kallo a matsayin kananan ‘yan takara a zaben shugabancin Faransa, na ci gaba da samun karuwar farin jinni a tsakanin al’ummar kasar biyo bayan maharawar da aka yi a tsakanin mutane 11 da ke takara a wannan zabe da za a yi ranar 23 ga wannan wata na Afrilu.

Maharawar da aka yi a tsakanin mutane 11 da ke takara a Faransa
Maharawar da aka yi a tsakanin mutane 11 da ke takara a Faransa REUTERS/Lionel Bonaventure
Talla

A cikin kwanaki 17 ma su zuwa ne za a gudanar da zagayen farko na zaben shugabancin kasar ta Faransa, inda kowane daga cikin ‘yan takarar ke kokarin gamsar da masu kada kuri’a.

Sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka fitar jim kadan bayan kammala mahawarar a cikin daren talatar da ta gabata, na nuni da cewa Jean Luc Melechon na jam’iyyar masu ra’ayin kominisanci ne ya fi samun karuwar farin jini sakamakon furta kalamai masu gamsarwa lokacin mahawarar.

Batun yaki da ta’addanci da kuma makomar Faransa a kungiyar Turai, kusan su ne suka fi daukar hankulan ‘yan takarar, to sai dai sabanin yadda aka saba gani, a wannan karo ‘yan takara daga manyan jam’iyun siyasa da suka hada da Francois Fillon da kuma Marine Le Pen, sun fi shan kakkausar suka ne daga Philippe Poutou, wanda lebara ne a kamfanin kera motoci na Ford amma kuma ya ke takara a zaben.

Akwai sauran ‘yan takara a wannan zabe da suka hada da Emmanuel Macron da kuma Benoit Hamon, wadanda ba su samu wani sauyi dangane da matsayin da suke da shi kafin wannan mahawara ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.