Isa ga babban shafi
Faransa

Macron ya soki manufar Le Pen kan tattalin arziki.

‘Yan takarar zaben shugabancin Faransa 11, sun fafata a mahawarar da suka tafka dan janyo hankalin masu kada kuri’a a zaben da za’ayi ranar 23 ga wata.

'Yan takarar shugabancin Faransa, yayin muhawarar da ta gudana a daren Talata.
'Yan takarar shugabancin Faransa, yayin muhawarar da ta gudana a daren Talata. 路透社
Talla

Dan takarar dake sahun gaba Emmanuel Macron ya soki Marine Le Pen kan shirin ta na tattalin arziki da kuma soke amfani da kudin euro.

Mahawara lokaci zuwa lokaci ta kan yi zafi tsakanin yan takarar 11, wadanda ke goyan bayan jari hujja da kuma masu adawa da kungiyar kasashen Turai.

Abinda ya fi daukar hankali shi ne lokacin da Emmanuel Macron ya kalubalanci Le Pen dangane da shirin ta na soke amfani da kudin euro dan komawa amfani da Ceaf Franc.

Macron ya shaida mata cewar, shirin na ta wani yunkuri ne na rage karfin cinikayyar da Faransawa keyi, musamman ma’aikata da kuma raba mutanen kasar da takwarorin sun a Turai.

A gefenta kuma, Le Pen ta bayyana fargaba ce kan yadda ake samun durkushewar kamfanoni da kuma barazanar yan ta’adda.

Dan takarar Socialist Benoit Hamon ya bayyana damuwa kan harin da ake kaiwa baki, yayin da Jean-Luc Melenchon ya taka rawa sosai a mahawarar.

Shi kuwa, Francois Fillon yace idan dai masu kada kuri’a na bukatar kaucewa barazanar dake fuskantar Faransa sakamakon aniyar Le Pen, toh shi yafi dacewa a zaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.