Isa ga babban shafi
Faransa

'Yan takarar Faransa 11 za su tafka muhawara a yau

Yau ake saran 'yan takarar shugabancin Faransa 11 za su sake tafka wata mahawara dan bayyana manufofinsu ga al’ummar kasar, yayin da ya rage kasa da makwanni uku a gudanar da zabe.

Wasu daga cikin 'yan takarar shugabancin Faransa da za su tafka muhawara a dern yau Talata
Wasu daga cikin 'yan takarar shugabancin Faransa da za su tafka muhawara a dern yau Talata Eliot BLONDET / AFP
Talla

Dan takarar Jam’iyyar Socialist Benoit Hamon ya tura wata tawaga uku don karade garuruwa 100 don fatar ganin sun janyo hankulan jama'a don kada kuri'a ga Jam’iyyar.

A bangare daya kuma wasu masu shirin fina-finai da makada 100 sun wallafa wata wasika da suke bukatar 'yan kasar da su kaurace wa zaben Marine Le Pen mai matsanancin ra'ayin kishin kasa.

Mutanen sun ce, zaben Le Pen zai hana su 'yancin gudanar da ayyukansu da kuma kawo karshen 'yancin da aka san kasar da bai wa jama’a.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.