Isa ga babban shafi
Faransa

Ministan cikin gidan Faransa ya ajiye aikinsa

Ministan cikin gidan kasar Faransa Bruno Le Roux ya sauka daga mukaminsa, sa’o’i kadan bayanda babban lauyan gwamnatin kasar, ya sanar da fara bincike kan zargin badakalar ayyukan bogi da ake wa ministan, na baiwa yayansa mata mukaman mataimakansa a majalisar dokokin kasar, a lokacin da yake dan majalisa.

Ministan cikin gidan Faransa Bruno Le Roux.
Ministan cikin gidan Faransa Bruno Le Roux. REUTERS/Charles Platiau/File Photo
Talla

Wani shirin talibijin din TMC na ranar jiya Litanin ne ya bayyana cewa Bruno Le Roux, ya bai wa yayansa mata 2 kwangilar aikin Euro dubu 55,000 a matsayin mataimakansa a majalisar dokoki, yayinda ‘ya’yan nasa ke makarantar share fagen shiga jami’a, tsakanin shekarun 2009 da 2016, a lokacin suna ‘yan shekaru 15 da 16 a duniya.

Wannan badakalar dai ta dauki hankula sosai a Faransa, sakamakon makamanciyarta da ake zargin mai ra’ayin rikau, haka kuma dan takarar jam’iyyar Republican ta ‘yan adawa François Fillon da ita, na bawa matarsa aikin bogi na mataimakiyarsa a harkokin majalisar dokoki a lokacin da yake rike da mukamin Firaministan kasar daga shekarar 2008 zuwa da 2012.

Yanzu haka dai lauyan gwamnatin Faransa, mai binciken badakalar kudi ya saka Bruno Le Roux, a jerin takwarorinsa da yake zargi da irin wannan laifi da suka hada da François Fillon da kuma uwargida Marine Le Pen, da ita ma ake zargi da bada aikin bogin, amma ita nata a majalisar dokokin kungiyar tarayyar turai EU.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.