Isa ga babban shafi
Paraguay

Masu zanga zanga a Paraguay sun bankawa ginin majalisar kasar wuta

Masu zanga zanga a kasar Paraguay, sun cinnawa ginin majalisar dokokin kasar wuta, bayanda zanga zangar ta juye zuwa tarzoma, sakamakon adawa da dubban al’ummar kasar ke yi da kudurin da zai sauya wa’adin shugabancin kasar.

Ginin majalisar kasar Paraguay da masu zanga zanga suka bankawa wuta.
Ginin majalisar kasar Paraguay da masu zanga zanga suka bankawa wuta. REUTERS/Jorge Adorno
Talla

Mutane 30 ne suka samu munanan raunuka sakamakon tashin hankali ciki harda ‘yan majalisar wakilai uku da kuma sanata guda, yayinda wani dan fafutuka daga bangaren ‘yan adawa Rodrigo Quintana mai shekaru 25
ya rasa ransa sakamakon raunin da ya samu a kai.

‘Yan adawa sun dora laifin kisan, kan ‘yan sanda da ke harbi kan masu zanga zangar da alburushin roba.

Tsarin mulkin kasar Paraguay dai ya bai wa shugaban kasa damar yin wa’adi daya ne kawai, tsawon shekaru biyar, to sai dai shugaban kasar Horacio Cartes ya mikawa majalisar kasar kudurin yiwa kundin tsarin mulkin kwaskwarima don samun damar yin tazarce.

Karo na farko kenan, da irin wannan tarzomar da ta haifar da arangama tsakanin ‘yan sanda da al’ummar gari ke faruwa a kasar ta Paraguay tun bayan komawa tsarin Dimokaradiyya a shekara ta 1992.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.