Isa ga babban shafi
Paraguay

Ana gudanar da zaben shugaban kasa na 'yan Majalisa a Paraguay

Ana gudanar da zaben shugaban kasa da na Majalisar Dokoki a kasar Paraguay a yau lahadi, inda a neman shugabancin kasar ake karawa tsakanin ‘yan takara masu bambancin ra’ayin siyasa Horacio Cartes mai tsautsauran ra’ayi da kuma Efrain Alegre na jam’iyyar mai sassaucin ra’ayin da ke goyon bayan salon jari hujja.

Ofishin jam'iyyar Colarado a Paraguay
Ofishin jam'iyyar Colarado a Paraguay REUTERS/Jorge Adorno
Talla

Kuri’ar ra’ayin jin jama’a da aka gudanar kafin yau, na nuni da cewa Haracio Cartes ne ke sahun gaba a farin jinni, to sai dai a tsawon shekaru 60 da suka gabata, jam’iyyar Colarado ce ta Efrain Alegre ke mulki a kasar, to amma kuma a yau dan takararta ya kasa samun yardar jama’ar kasar.
Shi kuwa Horacio Cartes, wanda ake kira da suna « Berlusconi na Paraguay », ya yi karantunsa ne a kasar Amurka, kuma hamshakin attajiri ne. Ya dai gudanar da yakin neman zabensa ne ta hanyar daukar alkawalin kara janyo masu saka jari zuwa kasar matukar dai aka zabe shi a matsayin shugaban kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.