An kama mutane 4 da ke shirin kai harin ta'addanci
‘Yansanda a Faransa sun cafke wasu mutane 4 ciki har da wata yarinya mai shekaru 16 da ake zargi da shirin kitsa kai harin ta’addanci a cikin kasar.
Wallafawa ranar:
Ministan harkokin cikin gidan kasar Bruno Le Roux ne ya tabbatar da hakan inda ya ce ‘yansanda sun kama mutanen ne a birnin Montpellier.
Sanarwara ta kara da cewa ‘yansandan sun cafke mutanen ne a lokacin da suke kokarin siyan wani sinadari da ake amfani da shi wajen hada abubuwan fashewa a wani shago.
Sauran wadanda aka cafken maza ne da ke da shekaru tsakanin 20 zuwa 33 inda yanzu ake ci gaba da gudanar da bincike a kansu.
Faransa na fuskantar hare-haren ta’addanci a baya bayan nan al’amarin da ya sa gwamnatin ta tsaurara matakan tsaro don kaucewa aukuwarsu.
A bara mutane fiye da dari daya ne suka mutu a jerin harin ta’addanci da aka kai a Faransa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu