Isa ga babban shafi
Faransa

An yi wa matar da ta kashe mijinta afuwa

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya yi wa Jacqueline Sauvage afuwa, matar da ta amsa laifin kashe mijinta sakamakon azabar da ta sha a hannunsa.

Jacqueline Sauvage ta kashe mijinta a shekarar 2012
Jacqueline Sauvage ta kashe mijinta a shekarar 2012
Talla

A farkon watan janairu ne shugaba Hollande ya soma bayar da umarni yi wa Jacqueline Sauvage afuwa bayan an yanke mata hukuncin zaman gidan yari na shekaru goma bisa laifin kashe mijinta na shekaru 47.

A sanarwar da shugaba Hollande ya fitar da ke dauke da umarnin yi wa Sauvage afuwa, Hollande ya ce ya kamata ta kasance da iyalanta maimakon zaman gidan yari.

A shekarar 2012 aka sami Sauvage da laifin kisa bayan da ta amsa harbin mijinta Nobert Marot har sau uku, kwana guda bayan da dansu ya kashe kansa.

A lokacin shari’ar, Sauvage ta yi wa kotu bayanin rayuwarta da mijin da ta ce ya azabtar da ita da ‘ya’yansu da kuma yi musu fyade.

Uku daga cikin yaran matan sun tabbatar wa kotu yadda mahaifin na su ya sha yi musu fyade baya ga azabar da ya gallaza musu.

Wannan batun na Jacqueline Sauvage dai ya matukar jan hankulan al’ummar kasar inda aka sami mutane fiye da dubu hudu da suka sanya hannu kan wata takarda kan sakin matar mai shekaru 60 a duniya.

Kundin tsarin mulkin Faransa ya bai wa shugaban kasa damar yi ma mai laifi afuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.