Isa ga babban shafi
Malawi

Shugaban Kasar Malawi Yayiwa Fursunoni 287 Afuwa

Shugaban kasar Malawi Bingu wa Mutharika ya yafewa fursunoni 287, yau domin murnan cikan kasar shekaru 46 da samun ‘yancin kai daga kasar Britaniya.Ma'aikatar tsaro dake kasar ta fadi cikin wata sanarwa cewa wadan da akayi wa afuwan yawanci sun kwashe rabin yawan shekarun da zasu yi a gidan yari, wasu kuma anyi masu ne saboda nuna halaye masu kyau.Shugaban kasar Malawi ya saba yin afuwa ga fursunoni a lokuttan bukukuwan kirsimati ko na samun ‘yancin kai.Kasar Malawi nada gidajen yari 30 dake tsare da masu laifuka 12,500.Mutane 5,500 ne ya kamata suna tsare a gidajen yarin kasar.Shugaban kasar na wa'adinsa na biyu ne da zai kare cikin 2014.Kasar Malawi ta kasance daya daga cikin mafi talauci a duniya, gashi kuma cutar kanjamau tayi ta'adin gaske inda mutane akalla miliyan daya ke fama da cutar. 

Shugaban Malawi, Bingu  wa Mutharika.
Shugaban Malawi, Bingu wa Mutharika. rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.