Isa ga babban shafi
Amurka

Turai ta haramta sayan nama daga Amurka da aka sauyawa halitta

Kasar Amurka ta bayyana bacin ran ta da matakin da kungiyar kasashen turai ta dauka na haramta shiga Yankin da naman shanun da aka sauyawa halitta daga Amurka.

Talla

Sakataren kula da ayyukan noma, Tom Vilsack yace manoma Amurkawa na samar da nama mafi inganci a duniya, amma dokokin kasashen Turai na hana sayar da naman a yankin cikin farashi mai sauki.

A shekara ta 1998 kungiyar cinikayya ta duniya ta bayyana haramcin kungiyar kasashen Turan a matsayin wanda ya saba ka’ida.

Masu sa ido na hasashen cewar Amurka na iya mayar da martini wajen sanya haraji kan kayan da akeyi a Turai, ake kuma shigar da su kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.