Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya gana da sojin Amurka kan jirgin F-35

Zababben shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump, ya gana da manyan jami’an sojin kasar don tattaunawa kan batun rage tsadar kudaden kera jiragen yaki, samfurin F-35. Wannan na zuwa ne bayan Trump ya nuna damuwa kan shirin kera jiragen da zai lakume kusan Dala biliyan 400.

Samfurin jirgin F-35
Samfurin jirgin F-35 Reuters/路透社
Talla

Trump ya gana da manyan jami’an sojin ne a jihar Florida, kuma hakan na zuwa ne mako guda da zababben shugaban ya caccaki tsadar shirin mallakar jiragen a shafinsa na Twaitter.

Masu mukamin Janar-Janar da kuma Admiral da suka hada da shugaban shirin kera jiragen, Laftanar Janar Christopher Bogdan, na cikin mahalarta tattaunawar ta jiya.

A lokacin da aka tambaye shi game da muhimmacin zaman, Mr. Trump cewa, ya yi, kokari suke yi don ganin an sassauta tsadar.

An dai kiyasta Dala biliyan 379 a matsayin kudaden da za a kashe wajen kera jiragen guda dubu 2 da 443, abin da zai kasance adadi na kudi mafi yawa da aka kashe don mallakar wani jirgi a tarihin duniya.

Kazalika an kiyasta cewa, a jumulce, jiragen za su lakume zunzurutun Dala Tiriliyan 1.da rabi, idan aka hada da kudaden kula da su har zuwa shekarar 2070.

A ranar 6 ga watan Disamban nan ne, Mr. Trump ya caccaki shirin mallakar sabon jirgin shugaban kasa Airforce One saboda kudin da zai lakume da ya kai Dala bilyan 4, abin da Trump bai gamsu da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.