Isa ga babban shafi
EU-Canada

Belgium ta gargadi Matsin lamba kan kulla kasuwanci da Canada

Yankunan Kasar Belgium da suka ki amincewa da shirin yarjejeniyar kasuwanci tsakanin kungiyar kasashen Turai da Canada sun ce babu matsin lambar da zai tirsasa su.

Yankunan Kasar Belgium sun bijirewa yarjejeniyar kasuwanci tsakanin EU da Canada
Yankunan Kasar Belgium sun bijirewa yarjejeniyar kasuwanci tsakanin EU da Canada Agencja Gazeta/Kuba Atys/via REUTERS ATTENTION EDITORS
Talla

Shugaban Yankin Wallonia, Paul Magnette ya ce ya zuwa yanzu sun samu gargadi har sau uku, saboda haka muddin suka samu na hudu za su kauracewa duk wata tattaunawa kan batun.

Da farko dai gwamnatin tarayyar kasar, da lardin da mazaunansa ke amfani da harshen Jamusanci da kuma wani yankin da ake amfani da harshen Flands, dukkaninsu sun amince a sanya hannu kan wannan yarjejeniyar mai suna CETA, to amma hukumomi a lardin Brussels da kuma sauran lardunan da ke magana da harshen Faransaci suka ce atattau.

Gobe ne ake saran sanya hannu kan yarjejeniyar tsakanin Firaministan Canada da wakilan kasashen Turai a Brussels, idan Belgium ta bada goyan baya.

Ita dai wannan yarjejeniya mai suna CETA, matukar aka amince da ita, to za ta kasance babbar kasuwar cinakayya da za ta kunshi sama da mutane milayn 500 wato mafi girma a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.