Isa ga babban shafi
Paris

An cimma yarjejeniya kan rage gurbatar muhalli

 An cimma matakin da ake ganin zai bada damar aiwatar da yarjejeniyar rage gurbatar muhallin da aka kulla a birnin Paris na kasar Faransa sakamakon amincewar 'yan Majalisar Kungiyar Kasashen Turai.

Shugaba Hollande da Ban Ki-moon na nuna farin cikin cimma yarjejeniya kan rage gurbatar yanayi
Shugaba Hollande da Ban Ki-moon na nuna farin cikin cimma yarjejeniya kan rage gurbatar yanayi
Talla

'Yan Majalisa 610 suka goyi bayan yarjejeniyar, yayin da 38 suka ki, 31 kuma suka ki kada kuri’a.

Wannan dai ya bude kofar baiwa kungiyar damar mikawa Majalisar Dinkin Duniya rahotan dan fara aiki da ita bayan wata guda.

Sakatare Janar na Majalisar dinkin Duniya Ban Ki Moon ya bayyana farin cikin sa da matakin.

Kasashen Duniya na kokarin ganin sun rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli ganin illolin da hayakin ke haifarwa ga yanayida kuma rayuwar dan'adam.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.