Isa ga babban shafi
China

China ta kaddamar da yaki da gurbatar yanayi

Firmiyan kasar China, Li Keqiang yace lokaci ya yi da za a kaddamar da yaki akan gurbatar yanayi a kasar, yana mai cewa akwai alamun gazawa wajen yaki da wannan matsala. Kasar China, ta samu bunkasa a fannin manyan masana’antunta, lamarin da masu kula da kiwon lafiya suka ce ya taimaka wajen haifar da mummunan yanayi a kasar da ke barazana ga lafiyar mutane.

Taron Majalisar kasar China
Taron Majalisar kasar China REUTERS/Jason Lee
Talla

A cikin jawabin da ya gabatar a zaman taron Majalisar na shekara da aka bude, Firimiya Li Keqiang yace suna fatar samun ci gaba da kashi 7.5.

Mista Li yace ci gaban tattalin arzikin China shi ne babban abinda gwamnatinsu zata saka a gaba.

A yau Laraba ne aka bude zaman taron Majalisar mai wakilai kimanin 3,000 daga sassan kasar China. Kuma shekara guda ke nan da aka tabbatar da Xi Jinping a matsayin shugaban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.