Isa ga babban shafi
Faransa

Sarkozy zai gurfana a gaban kotu

Bayan da ya saka kansa a cikin gawurtatar sukuwar neman shugabanci a zaben shugabancin kasa na shekara ta 2017 tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy na shirin gurfana a gaban kotu.

Nicolas Sarkozy na Faransa
Nicolas Sarkozy na Faransa REUTERS/Gonzalo Fuentes/File Photo
Talla

A cikin watan Agustan da ya gabata ne mai shigar da karar birnin Paris ya bayyana aniyar gurfanar da tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy a gaban kotun, tare da wasu makarabansa 13 da ake zargi da karbar kudade ba kan ka’ida ba, a yakin neman zabensa na shekara ta 2012

Shi dai Sarkozy, tun a cikin watan fabrairun wannan shekara ne, aka fara bincikensa kan zargin wuce mizanin kudaden yakin neman zaben da dokar kasar ta kayyadewa dan takara, tare da ya boye gaskiyar abinda ya kashe a cewar majiyar.

Nan take dai Lauyan dake kare shi Me Thierry Herzog, ya musanta zargin da ya danganta da wani sabon mummunan bita da kullin siyasa da ake yi masa.

Yanzu dai maganar karshe kan wannan badakalar ta na ga alkalan dake wannan shara’ a ne. Da za ta iya daukar wa’adin wata guda nan gaba kafin a fara ta kamar yadda mai shigar da karar gwamnatin ya bukata

Wannan kuma zai baiwa bangarorin biyu, dama gabatar da shaidun da suke dasu, da kuma zai iya kara tsawaita wa’adin.

Haka kuma kotun na iya korar shara’ar dai zai sa tsohon shugaban Sarkozy isa barka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.