Isa ga babban shafi
Faransa

Hollande zai fuskanci sabuwar Hamayya a Faransa

Fadar shugaban kasar Faransa ta tabbatar da murabus din Ministan bunkasa tatalin arzikin kasar Emmanuel Macron.

Shugaban Faransa Francois Hollande
Shugaban Faransa Francois Hollande REUTERS/Clodagh Kilcoyne
Talla

Macron ya ajiye aiki ne domin samun damar tsayawa takara a zaben shugabancin kasar Faransa na 2017 mai zuwa.

Matashin ministan dan shekaru 38 a duniya, a safiyar talata ya sanar da zai gabatar da murabus dinsa kamar yadda majiyoyi da dama suka tabbatar, inda kuma nan take ya nufi fadar L’Elysee ya kuma gabatarwa shugaban Francois Holland takardar murabus din nasa

Murabus din dai ya zama koma baya ga Francois Hollande, wanda zai kara fuskantar sabon abokin hamayya a gudun yada kanin wani yayin neman jam’iyar socialiste ta tsayar da su takara a zaben shugabancin kasar na 2017.

Emanuel Macron yana daga cikin ministocin da aka fi yabawa da ayukansu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.