Isa ga babban shafi
Amurka

Matakan Trump kan Ta'addanci bayan cin zabe

Dan takarar Shugabancin Amurka karkashin Jam'iyyar Republican Donald Trump ya bayyana matakan da zai dauka na yakar ta’addanci, masu tsattsauran ra’ayi da kuma dakile kwararar ‘yan gudun hijira idan har ya ci zaben shugaban kasa. 

Dan takarar shugabancin Amurka a Republican Donald Trump
Dan takarar shugabancin Amurka a Republican Donald Trump REUTERS
Talla

A wani jawabin da ya gabatar kan manofofin gwamnatinsa idan har ya zama shugaban Amurka Donald Trump ya ce za a dakatar da bawa ‘yan kasashen da ke fama da matsalar hare haren ta’addanci izinin shiga Amurka.

Trump ya gabatar da jawabin ne a Ohio, inda ya ce zai hada hannu da kasashen da suka ga suna iya taimakawa Amurka yakar IS.

A cikin jawabin ya ce zai kuma tsaurara bincike musamman tambayoyi na gwajin akida ga duk wani bakon haure ko dan gudun hijira da ke son shiga Amurka.

A baya Trump ya ce zai haramtawa musulmi shiga Amurka. Kuma a yakin neman zabensa ya ce zai hana 'yan kasashen Turai da ke fama da hare haren IS shiga Amurka da suka hada da Faransa da Belgium da Jamus.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.