Fira Ministan Britaniya ya yi gargadi a guji nuna kyamar baki
Fira Ministan kasar Britaniya David Cameron ya gargadi mutan kasar da su guji nuna duk wata kyamar baki bayan da aka yi zaben raba-gardama dake nuna an fi kaunar ficewa daga cikin kungiyar Tarayyar Turai.
Wallafawa ranar:
Fira Minista David Cameron wanda yake Magana da manema labarai ta bakin kakakin sa , ya ce Gwamnatin Britaniya ba zata amince da muzgunawa baki ba, da wasu ‘yan son iyawa suka fara nunawa.
A dan tsakanin nan ne Ofishin jakadancin Poland a Landan ya bayyana damuwa saboda wasu kalamai da takala da ake yi wa al'ummar Poland mazauna Landan.
Acewar Ofishin Jakadancin Poland a Landan wasu har aike masu da wasiku suke yi ana zolayansu wai su koma 'kasar EU ba kasar Britania ba'.
Magajin garin birnin Landan Sadiq Khan tuni dai ya sanar da jami'an tsaro domin ganin sun sa ido kada wasu su janyo tarzoma a kasar.
Jami'an tsaro a Landan sun bayyana cewa suna nazarin irin wasiku da wasu suka rubuta inda suke nuna kyamar baki bayan zaben raba gardama da aka gudanar makon jiya.
Shi kansa Ministan kudi na Britania George Osborne ya ja kunnen masu nuna kyamar baki inda yake cewa Britaniya ba'a san ta da nuna kyama ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu