Maharin Brussels ya taba aiki a Majalisar Turai
Wani Bincike a Turai ya nuna cewar daya daga cikin mutanen da suka kai harin bam a Brussels wanda ya hallaka mutane 32 ya taba aiki a Majalisar kungiyar kasashen Turai.
Wallafawa ranar:
Mai magana da yawun Mjalaisar, Jaume Duch Guillot, ya ce Maharin mai shekaru 25, ya yi aiki a matsayin mai shara a 2009 a karkashin wani kamfanin da aka bai wa kwangilar tsabtace Majalisar.
Sai dai ba a bayyana sunan shi ba, amma wata majiya kusa da masu bincike tace sunan maharin Najim Laachraoui.
Kakakin ya ce a lokacin da ya yi aiki babu wani tarihi akan shi na aikata laifi, amma ya tafi Syria a 2013.
Ana kuma zargin Najim Laachraoui yana da alaka da hare haren da aka kai a birnin Paris a watan Nuwamba inda aka kashe mutane 130.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu