Isa ga babban shafi
Faransa

Batun hana sanya hular Yahudawa ya janyo muhawara a Faransa

Ana ci gaba da cece kuce game da batun da shugaban Yahudawan Faransa ya yi kan sauya kamanni wajenu dakatar da saka hular nan da suke sanya wa a kokuwar kai, don kaucewa hari.

Yahudawa na fuskantan barazana a Faransa bayan harin Marseille.
Yahudawa na fuskantan barazana a Faransa bayan harin Marseille. AFP / Boris Horvat
Talla

Shugaba Hollande ya ce babu dalilin da zai sa Yahudawan boye kamanninsu saboda tsoron farmaki.

A cewar shugaba Hollande ko kadan bai kamata yahudawan Faransa su razana ba a matsayinsu na ‘yan kasa saboda Fargabar hari sakamakon zabin addininsu.

Tuni dai aka fara cecekuce bisa furucin shugaban yahudawan na Faransawanda ya yi kiran duk wani Bayahude ya dakatar da saka hular don boye kamannin su na addini.

Tuni wasu iyaye a garin Marseille da aka kai wa wani Bayahude hari suka fara umartar ‘ya’yansu da su koma saka hular ‘yan kwallon baseball don kariyar kai daga hari.

Wani matashi ne dai dan shekaru 15 da aka ce dan kasar Turkiya ne ya kai wa wani Bayahude hari a ranar Litinin ta hanyar daba masa wuka.

Amma sai dai matashin ya shaidawa masu bincike cewa ya yi takaici matuka da bai hallaka Bayahuden ba.

Tuni dai gwamnatin Faransa ta bakin mai magana da yawunta Steffane Le Foll ta yi allawadai da harin tana mai cewa ana neman dawo da bara bana ne kawai ga batun al’adar kyamatar Yahudawa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.