Isa ga babban shafi
Faransa

Shekara guda da harin Charlie Hebdo

Kasar Faransa ta fara bikin cika shekara guda da jimamin harin da aka kai wa mujallar Charlie Hebdo a ranar 7 ga watan Janairu inda aka kashe mutane 17.Shugaban Faransa ya ziyarci tsohon ginin mujallar a yau Talata da aka soma bikin na cika shekara guda.

Shugaban kasar Faransa François Hollande, da tawagarsa a ginin Mujallar Charlie Hebdo
Shugaban kasar Faransa François Hollande, da tawagarsa a ginin Mujallar Charlie Hebdo AFP PHOTO / KENZO TRIBOUILLARD
Talla

Shugaba Hollande na Faransa ya kaddamar da bikin jimamin ne a yau a ginin mujallar Charlie inda aka kafa wasu alluna da ke dauke da sunayen ma’aikatan jaridar da aka kashe.

Wannan ne dai karon farko da aka soma bikin na tuna harin Cherlie inda wasu ‘yan uwan juna Said da Cherif Kouachi suka kai hari a ranar 7 ga watan Janairu.

Harin kuma ya samo asali ne daga wani zanen da mujallar ta yi da aka danganta da fiyayyen halitta.

Kuma tun daga lokacin Faransa ke fuskantar barazanar hare hare inda a ranar 13 ga watan Nuwamba aka kashe mutane 130 a munanan hare hare da aka a birnin Paris

Kungiyar IS da ke da’awar jihadi ta yi ikirarin daukar alhakin kai harin.

Yanzu kuma a yayin bikin, an shirya buga mujallar ta Cherlie mai zanen barkwanci, wanda wasu ke ganin sai Faransa ta yi taka tsan-tsan da abinde ke kunshe a mujjalar don gudun sake kai wa kasar hari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.