Isa ga babban shafi
Faransa

An cafke mutane da dama bayan hare-haren birnin Paris

A ci gaba da bincike domin gano wadanda ke da hannu a hare-haren ta’addancin da aka kai birnin Paris cikin daren juma’ar da ta gabata, hukumomi a Faransa sun ce yanzu haka suna tsare da mutane biyu ‘yan uwan daya daga cikin maharan mai suna Omar Ismael Mostefai wanda aka haifa a wata unguwar birnin Paris kimanin shekaru 30 da suka gabata.

Mutanen da suka sami raunuka a Bataclan 13 nuwamba 2015
Mutanen da suka sami raunuka a Bataclan 13 nuwamba 2015 KENZO TRIBOUILLARD/AFP
Talla

Mai shigar da kara na gwmanatin Faransa ya ce ana tsare da mahaifi da kuma yayansa maharin wanda ya tarwatsa kansa a lokacin harin.

Hakazalika masu bincike sun ce sun gano inda maharan suka yo hayar daya daga cikin motocin da ‘yan ta’addar suka yi amfani da su wajen kai harin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.