Isa ga babban shafi
Najeriya-Faransa

Harin Paris: Buhari ya jajantawa Faransa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi allawadai da hare haren da ‘Yan ta’adda suka kai a Paris inda mutane da dama suka mutu, Shugaban ya bayyana kaduwarsa da bakin ciki a lokacin da ya ji labarin hare haren da ‘Yan ta’adda suka kaddamar a Paris.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AFP via telegraph
Talla

A cikin wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya fitar, Sanarwa ta fadi cewa gwamnatin Buhari da al’ummar Najeriya na jajatawa shugaban Faransa François Hollande da al’ummar kasar, musamman iyalan wadanda hare haren na birnin Paris ya rutsa da su.

Tun a jiya Juma’a ne dai shugabannin kasashen duniya ke jajatawa Faransa tare da aike wa da sakon yin allawadai da hare haren da ‘Yan ta’adda suka kai a Paris.

Kasashen larabawa a yankin Gulf sun yi allawadai da jerin hare haren da ‘Yan ta’adda suka kai a Paris inda aka kashe mutane akalla 128 tare da raunana 300. Kasashen daular Larabawa da Saudiya da Qatar da Bahrain sun jajantawa Faransa tare da yin allawadai da hare haren.

Majalisar manyan malamai a daular Larabawa ta yi allawadai da harin wanda ta ce ya sabawa karantarwar addinin Islama.

Haka ma shugabannin Isra’ila da Falasdinawa sun yi allawadai da hare haren na Faransa.

A sakon da ya aika wa Faransa, Firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu ya ce yana tare da al’ummar kasar yayin da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya bayyana kaduwarsa da bakin cikinsa.

A yau Assabar dubban mutane ne suka hada gangami a biranen Tel Aviv da Ramallah domin nuna goyon baya ga Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.