Kasashen Turai sun tsaurara tsaro a manyan biranensu
Hukumomin Turai sun tsaurara matakan tsaro a manyan biranensu kuma gwamnatocin kasashen sun gudanar da taron gaggawa na ministocinsu a yau Assabar domin tattauna matakan tsaro bayan hare haren da ‘Yan ta’adda suka kai birnin Paris na Faransa.
Wallafawa ranar:
Firaministan Birtaniya ya ce zai sake nazari akan tsaron kasa bayan ya gana da ministocinsa.
Shugabannin kasashen Jamus da Italiya da Spain da Austria sun gana da ministocinsu a yau Assabar kan sha’anin tsaro bayan harin Paris.
Ministan harakokin wajen Faransa Laurent Fabius ya ce sun tsaurara matakan tsaro a ofishoshin jekadanci da gine ginen kasar a sassan kasashen duniya, bayan jerin hare haren da ‘Yan ta’adda suka a birnin Paris.
Tun a daren juma’a ne da ake kai hare haren Paris, Shugaba Hollande ya kafa dokar dokar ta-baci a Faransa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu