Isa ga babban shafi
Faransa

Kasashen duniya sun yi tir da hare-haren ta'addanci a Paris

Kasashen duniya na ci gaba da jajantawa Faransa danagane da hare-haren ta’addanci da aka kai wa kasar, inda shugaban Amurka Barack Obama wanda ke zantawa da Francois Hollande ta wayar tarho, ya bayyana harin a matsayin wanda aka kai wa duniya ba wai Faransa kawai ba.

Zaratan dakarun Faransa na ceton juma'a a Paris
Zaratan dakarun Faransa na ceton juma'a a Paris 路透社
Talla

Hakazalika shugabannnin kasasashen duniya da suka hada da Rasha, Birtaniya, Jamus, Spain da kuma Italiya, dukkaninsu sun tir da wannan lamari, yayin da kasashen China da Japan suka bayyana alhininsu tare da bayyana ta’addancin a matsayin babbar barazana ga sauran kasashe na duniya.

Hari na daren jiya dai ya zo ne watanni 10 cur da kai wa mujallar Charlie Hebdo da kuma sauna hare-haren da suka biyo baya a birnin na Paris.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.