Isa ga babban shafi
Faransa

An karrama wasu ‘Yan jaridun aka kashe

Kungiyar Kare hakkin ‘Yan Jaridu ta Duniya, Reporters Without Borders ta sanya sunayen wasu ‘yan Jaridu 12 da aka hallaka a titunan birnin Paris.

MSF ta karrama Ghislane Dupont da Claude Verlon, ma’aikatan Radio France Internationale da aka kashe a Kidal
MSF ta karrama Ghislane Dupont da Claude Verlon, ma’aikatan Radio France Internationale da aka kashe a Kidal fr.rsf.org
Talla

Wata sanarwar da kungiyar ta fitar dangane da ranar yaki da cin zarafin ‘yan jaridu ta duniya, kungiyar ta nuna cewar an sanya sunayen ‘yan jaridun ne a titunan da kasashen su ke da ofishin jakadanci a birnin Paris domin karrama su da kuma neman ganin hukumomin kasashen da abin ya faru sun hukunta wadanda ake zargi.

Kungiyar ta bukaci jama’a da su taimaka wajen yaki da mutanen da ke abkawa ‘yan jaridu.

‘Yan Jaridun da aka karrama sun hada da Amir Kassir dan kasar Lebanon da Guy-Andre Kieffer dan kasar Faransa da Maria Esther Aguilar Cassimbe yar kasar Mexico.

Sauran sun hada da Sofiane Chourabi da Nadhir Ktari, yan kasar Tunisia da suka bata a Libya, sai kuma Ghislane Dupont da Claude Verlon, ma’aikatan Radio France Internationale da aka kashe a Kidal da ke kasar Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.