Isa ga babban shafi
EU-Hungary

Hungary za ta gina shinge saboda Bakin haure

Kasar Jamus ta bukaci Kungiyyar Turai ta shirya wani taro domin tattaunawa kan matsalar kwararar ‘Yan gudun hijira, yayin da Kasar Hugary ta rufe kan iyakarta da Serbia da nufin hana sabbin baki shiga Kasar.

REUTERS/Bernadett Szabo
Talla

An dai bayyana matsalar kwararar 'yan gudun hijira na wannan karan a Turai a matsayin mafi kamari tun bayan yakin duniya na 2 yayin da mutane 22 daga cikin su da ya hada da kananan yara da mata suka rasu a kan hanyarsu ta shiga Turai bayan kwale-kwalen da ya kwaso ya gamu da matsala a kan ruwa.

Shugabar gwamantin Jamus Angela Merkel ta gargadi cewa lokaci na kurewa kuma ta bukaci a gudanar da taron nan da mako mai zuwa domin tattauna yadda za a magance matsalar kwararar wadda ta kara tsananata bayan mambobin kasashen Turai da ke yankin gabashin nahiyar sun ki amincewa da karban wani kaso daga cikin 'Yan gudun hijirar.

A cewer Merkel wannan wata matsala ce da za su iya shawo kanta kuma tuni shugaban gwmanatin Austria da ke ziyara a Jamus Werner Faymann ya bada goyon bayansa game da gudanar da taron.

Jamus dai ta bukaci hukumar tarayyar Turai da ta katse duk wani tallafi ga kasashen da suka ki karban 'Yan gudun hijirar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.